WANI TABBACI DAGA SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H).
A ranar bikin Ghadeer, 18 ga Zulhijja, 1434 (22/10/2013), Shaikh Zakzaky (H) ya yi wani jawabi dangane da shirin maƙiya a kan nufinsu na ganin bayan Harkar Musulunci.
A ciki yana cewa:
“Maƙiyan gaskiyan na da, da na yanzu duk tafiyarsu daya ce, su basu da wani abu da za su yi illa kawai su yi tunanin bari su yi wani mugunta kawai. Shikenan zance ya kare.
"Za ku iya mugunta, bamu ce ba za ku iya ba, kuma za ku iya kisan kai, bamu ce ba za ku iya ba, tabbas kukan ma yi ma, kun ma kashe da yawa ma, kuma nan gaba ma za ku yi, amma abin da muka tabbatar har ga Allah shine, abin da duk za ku yi ba zai hana komai ba! Bilhasali ma zai mana kyau ne.
"Saboda haka ku ba da ƙoƙari, ba za mu ce kar ku yi ba. In baku yi ba ya fi muku alkairi, amma in kun yi kun cuci kanku, mu kuma babu abin da za mu yi illa mu koma ga Allah mu yi roko a kanku.”
Comments
Post a Comment