YA KAMATA KOWA YASAN DA WA YAKE MU'AMALA (true life story) daure ka karanta zai amfane ka.



Kwana 3 da suka shu'de wani mai siyar da wayoyi mai sana'a a PZ Zaria ya zo da wata waya kirar Samsung inda wani ma'koci na mai suna Musa ya shiga ciniki domin canja wanda yake hannun sa, Musa ya amshi waya domin gwada ta ko lafiyar ta lau ya saka Sim card din sa a ciki ya kira nambobi guda 2 domin tabbatar da lafiyar wayan kamar yadda aka saba.

Bayan ya kirayi wasu abokan kasuwancin sa sai aka fara cinikin wayan Samsung kirar S1 sai Allah ya nufa ba a daidai ta ba daga nan sai Musa ya cire Sim card din sa ya baiwa mai waya abun sa suka rabu.

Can zuwa Yamma sai aka aika a kira Musa a gidan sa wai yayi baqi, da fitowar sa sai ya ga police na jiran sa ko da ya tambaya lafiya, sai dan Sandan yace suje "station" zai bayani, daganan sai Musan ya dauki Police din a mashin dinsa zuwa Helkwata na en sanda dake PZ duk a birnin Zaria.

Aka tambayi Musa ina Wayan nan Kirar Samsung S1 da ya saka Layin shi awanni kadan dasu ka shude, yace ya baiwa Mai Shi abun sa, sai Dan Sandan ya ci gaba da cewa wannan waYan sato ta akayi bayan an sassari mai wayan yanzu haka yana kwance a Asibitin Leprosy, sannan an sace motan sa da kudi naira dubu 'dari takwas (800,000). Musa yayi Salati ya sanar da Ubangiji, taimakon sa 'daya yasan wanda ya bashi wayan ya siya aikuwa ya bayyana shi aka tafi aka kamo shi bayan anyi masa en dabarbaru.

Da aka tabbatar Musa bai da laifi sai aka bada belin sa akan naira dubu biyar (5k) sannan ya biya kudin "Tracking" bin kwakkwafin layi akan naira dubu shabiyar (15k) saboda an tabbatar cewa bai da laifi.

Ku duba ku gani gwada Layin waya (sim card) a wata wayan kawai ya ja masa wannan Asarar da kwana a police station ina ga kai mai tsintar layi ka saka, ko kuma mai arawa wani wanda baka sani ba wayan ka yayi waya ya dawo maka da ita!

 Sai mu kiyaye musan da wa muke mu'amala rayuwan nan cike take da marasa gaskiya.

Comments

Popular Posts