Rayuwar Mallam Zakzaky Na Cikin Hatsari A Gidan Yarin Kaduna
Bayan bincike munsamu tabbacin akwai abinda ke faruwa wayewan garin Talata a gidan yarin Kaduna inda Mallam Zakzaky da matarsa Mallama Zeenah suke tsare tsawon watanni!
Wani Shaidan gani da ido ya tabbatarmin cewa; yanzu haka mazauna gidan yarin suna ta ihu suna buga abubuwa suna fadin a sake su!
Wata majiyar da ban tabbatar ba har yayin wannan rubutun ta bayyana cewa; ana zargin wata mata daga shashin matan gidan tana dauke da cutar Corona, wanda ance an garzaya da ita Asibiti, inji majiyar.
Jami'an tsaron gidan yarin da hadin gwaiwn sojoj sun fara harbi a cikin gidan yayin da mazauna gidan ke ihun a sake su!
Koda babu maganan bullar Corona bata tabbata ba, amma de an tabbatar min ana hatsaniyya kuma suna harbi, lalle bamu da aminci da mutanen da sukaje har gida domin su kashe mu yanzu wata babban dama ce suka samu da tafi ta baya.
Lalle ne rayuwar Mallam Zakzaky tana cikin Hadari a wannan lokacin, koba komai munsan gidan yari gidane na cutuka koda ba masu yaduwa bane, sannan kuma Mallam din yana tattare da raununa masu nauyi a jikin shi.
Daga Bilya Hamza Dass
Comments
Post a Comment