YA KAMATA MU DAMU DA HALIN DA MALAM ZAKZAKY(H) DA MALAMA ZEENAT SUKE CIKI NE BA CECE-KUCE BA..


Koda babu raunuka da ciwo a jikin Malam Zakzaky(H) da Matarsa zamansu a gidan kurkuku alheri ne.?
Shin mun gaji da addu'a, Muzahara, gangami da rubuce-rubuce akan zaluncin da aka yiwa Malam Zakzaky(H) ne.?
Yaushe muke da lokacin rubuta matsalar da take tsakaninmu a social media.?
Wadanda suka kashe Mana 'yan-uwa sama da dubu kisa na wauta, jahilci, dabbanci da hauka suna nan suna kallonmu suna shirye-shiryen kaddamar rashin albarka akanmu,suna nan basu gajiya wurin shirya ta'addanci akan Malam Zakzaky(H)  da da'awarsa,mu kuwa muna nan muna hantara, zage-zage da cin mutuncin junanmu alhali jinanen 'yan-uwanmu da aka kashe basu gama bushewa ba...
Wallahi idan na tuna halin da Malam Zakzaky(H) yake ciki sannan na kuma ga yadda wadansu daga Almajiransa suna cece-kuce marar amfani akan matsalar da bata shafi cigaban Harkah ko 'yancin jagoransu ba,sai kawai na ji hawaye sun zubo min...
Malam Zakzaky(H) dai yace ba a rabuwa da matsala sai dai a koyi tafiya da matsalar, yaushe ne zamu daukar wa kanmu gyara matsalar da muma kanmu bangare ne na matsalar.?
Allahu Ta'ala ya bamu sabati da istikama,ya hada kan 'yan-uwa ya daukar Mana fansa ya Kuma gaggauta kwato Mana jagoranmu daga hannun azzalumai alfarmar Annabi Muhammadu(S) da Ahlulbaitinsa(AS)....

Comments

Popular Posts