Cikin Jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi a ranar Laraba

"Yanzu mutane sun zama kashi uku. Kashin farko sune; azzalumai. Kashi na biyu sune mu ‘yan kadan da muka tsaya muka fuskanci zalunci, sauran jama’a ‘yan kallo. Masu zura ido su ga, to, ya za ta kaya, tsakanin ‘yan kalilan (marasa karfi) da ‘yan kalilan (karfafa), wanda dukiyar kasa ke hannun su, makaman kasa ke hannun su, mulki na hannun su, amma suma kalilan ne. To, ya zata kaya tsakanin kalilan karfaffa da kalilan mara karfi, su kuma ‘yan zura ido ‘yan kallo ne. To, kiran mu ga masu ‘yan zura ido, shi ne; ko ku dauki bangare, ko kuma lazim kuna tare da azzalumai! Wanda duk ya ce; shi dan ba ruwansa ne, karya yake yana tare da azzalumai ne. Kuma in kiyama ta zo; lallai zai tashi tare da su ne. Domin wanda ya ga ana barna ya yi shiru, to yana tare da mabarnaci."

— Cikin Jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi a ranar Laraba
, 9 ga watan Zulka’ada, 1435, (4/4/2014), a muhallin Jannatul Darul Rahma dake Dambo a garin Zariya.

Comments

Popular Posts