ABIN LURA:
👇
A yayin da na yi wa wani Malami kuma Ubana yabo da jinjina a kan tsayuwarsu a kan wani al'amarin a tsawon shekaru a tafarkin addini.
Daga abin da ya biyo bayan tattaunawarmu da shi, ya kawo min wani Hadisi da ya nuna an samo shi daga cikin littafin Mishkatul Anwar, shafi na 312. Cewa hadisi ne mai matukar ban tsoro ga Mumini, wanda kuma Jagoranmu (H) ya sha karanta mana shi ta sigogi daban daban cewa:
An samo daga Ameerul Mu'uminina (AS) ya ce:
"—Duniya dukanta Jahilci ce, sai wuraren daukar Ilimi.
—Ilimi dukansa Hujja ne, sai wanda aka yi aiki da shi.
—Aiki dukansa Riya ne, sai wanda aka yi da Ikhlasi.
— Ikhlasi kuwa yana kan Hatsari ne, sai an jira an ga da me Bawa ya cika a karshen rayuwarsa."
Abin da nake tunawa yan uwana Muminai shine, "Iklasi" din nan abu ne mai matukar wahala da hadari. In mutum ya karanta babin Iklasi daga littafin Arba'una Hadis na Imam Khomeini, zai rika ganin anya kuwa zai kubuta daga shi? Domin misalin hatsarin Iklasi na iya aukuwa hatta a wannan abin da nake kokarin isarwa. Mai sauki ne Shaidan yace ka nuna musu cewa kai ba kowa bane, hakan zai sa su ganka a kowa din saboda za su dauka kana da Tawadi'u da Iklasi ne.
Don haka ma ban sani ba ko ruwaya ce, amma na tuna muna yara Malam Maina ya taba karantar da mu cewa ba kowane mai kokari ne ake yabonsa (musamman a gabansa) ba. Akwai sharuddan da ke sa a yabawa mutum a gabansa, daga ciki akwai samun natsuwa kan cewa wannan mutumin ya kai matakin da yabo da suka duk daya ne a wajensa.
Don haka a duk sadda aka ga wani nau'in kokari ko wani abu da yake sauke nauyi ne (ba ma lallai wani kokari bane) daga ba'amen mutum (irina), babban taimakon da dan uwa Mumini zai yi shine ya yi addu'ar alkairi da tabbata ga wannan mai sauke wajibin nasa, akan Allah kar ya gaji da shi, ya bashi tabbata, kuma ya karbi aikinsa.
Ni ina ga in ka rika koda mutum, tun yana jin shi ba komai bane, har shaidan yai amfani da wannan damar ya fara sa yana jin ai nine kaza, ai ni ke kaza, ai kaza da kaza ma... To, kamar an saka masa hannu ne wajen lalacewa.
Na sani, Hausawa kan ce yabon gwani ya zama dole, kuma dai ba a haramta yabon ba, don haka ne ma aka ruwaito cewa idan aka yabeka da wani abu, ka yi addu'a cewa: 'Ya Allah ka sanya na zama mafi alkairi daga abin da suke zato akaina, kuma ka yafe abin da basu sani ba na gazawata.' Amma akalla taimako ne da tausayawa ya zama ana sanin inda za a yi yabo, da marhalar da za a yi, da wanda za a yabawa din. A wasu lokuta maimakon zurfafa yabo ga mutum, a zabga masa addu'ar fatan alkairi da tabbata a tafarki, an fi taimakonsa. Ranshi ma zai fi jin dadi da amsa karamci sosai. Sabanin zurfafa yabo da ya kan sa mutum ya rika jin zargin kansa tunda ya san kan nasa.
Allah Ya datar da mu. Ya amintar da mu. Ya sa mu cika da imani akan aikin alkairi da Iklasi.

Comments
Post a Comment