FARIN CIKIN SU JAGORA DA YIN MUNASABA A ABUJA
Wata Rana a cikin ziyarori da ake kaiwa su Jagora (H), lokacin suna a hannun DSS. Ziyarar bayan Sallah din nan haka, ana baiwa su Jagora labarin munasabobi da abubuwa da aka yi, suka ji dadi, sai suka tambaya wasan Sallah na Fulani fa su ma sun yi a Abuja? Sai aka ce masu a'a, suka ce me yasa basu yi a can ba (Abuja)? Aka dai fada masu cewa ba a samu yi a can din ba dai. Su Jagora basu ji dadin rashin yin wannan Program a Abuja ba.
Bayan an dawo da Fulani suka ji abinda su Jagora suka fada, sai suka gyara, yan'uwa masu girma mu girmama duk abinda zai sa su Jagora farin ciki, mu yi kokarin kauce ma duk abinda zai bata Ran su Jagora komin kankantarsa, Allah (T) ya yi mana taimako.
Comments
Post a Comment