NA SHATA LAYIN RABUWA DA DUK WANDA KE GOYON BAYAN ZALUNCI DA AZZALUMAI!

Daga Ahmad Abdullahi Saminaka

A yadda ƙasarmu ta Najeriya take, mai cike da tarin mabanbanta addinai kala daban-daban, bai kamata don na fito na nuna ƙiyayyata ƙara-ra ga azzalumai waɗanda suka cuta mana ba tare da mun aikata masu laifin komai ba; sannan a lokaci guda kai a gefe guda can daban kazo kana yi mani ɓaɓatu da surutai na banza da wofi don ra'ayina ya banbanta da ra'ayinka, ni kuma na zura maka ido ina ci gaba da kasancewa tare da kai ba, ko kai wane ne kuwa! Shaikh Ibrahim Zakzaky (H) shine jagoranmu guda ɗaya tilo. Bamu da na biyunsa, shine kuma mutumin da a koda yaushe nake kwanana tare da baƙin cikin abin da aka yi masa na zalunci. Duk da cewa a wani janibi ɗin, ba abin baƙin ciki bane a wajensa. Ɗaukaka ce wanda Allah (T) ke yiwa manyan bayinsa, waɗanda suka cancanci hakan domin ɗaukaka matsayi da kuma darajarsu a cikin al'umma da kuma faɗin duniya baki ɗaya!

Allah (T) ya halicci zuciyar ɗan Adam ne akan son wanda ya kyautata mata, ita zuciya bata taɓa manta alkairin da aka aikata mata komai ƙanƙantarsa kuwa! Yaushe kake tunanin da har zuciyata zata taɓa mantawa da dukkan wani nau'i na zaluncin da azzalumai da wanda ya taimaka nasu wajen cutar da zuciyata? Idan har a tunaninka zuciyata zata karkato zuwa ga tausayi da halin da aka jefa zuciayata cikin tsanani da baƙin ciki, ɓacin rai da damuwa, yayi da zuciyata ke neman taimako da tausayawa ga dukkan wanda ke da 'insaniyya', anya. Kana ganin zan manta da gudunmawar da ya bada wajen cutar da zuciyata kuwa?

Ku sani, ina nuna ƙiyayyata ga duk azzalumin daya zalunci ni ne. A lokaci guda, kai kuma kana baƙin ciki da ɓacin ran wani mai ƙwaƙƙwaran dalilai da tarin hujjoji. Ka sani, babu ranar da ɓacin ranka zai taɓa yin tasiri a kaina! Idan kuma tunaninka shine, don mun saɓa a ra'ayi, fahimta ko bambanci a ɓangaren ibada ita ce gaɓar da ya kamata ka fito fili domin nuna maitarka a fili na rabuwa dani: ni a shirye nake na rabu da kowama waye!

Comments

Popular Posts