HAKKOKIN JAGORA AKAN MABIYA

Jagora na da hakkoki akan mabiyansa wadanda kiyaye wadannan hakkokin ke kara taimakon mabiyan zuwa ga hakikanin manufa da al'amari har fatansu ya tabbata. Da yawan lokaci mabiya su kan yi wani irin kuskure kamar misali idan mabiyi ya girma, sai ya dinga jin cewa shi yanzu ma ba sai ya yi duk abinda ake yi ba, ko kuma ma ya rika kallon masu yi din a wani kamanni na daban, yana ganin ai a baya ya yi wannan saboda haka ya wadatu da abinda ya aikata a baya.

Wani lokacin kuma idan mabiyi ya girma ya kan ga cewa yanzu fa duk abinda za ayi sai da shawararsa saboda yanzu ya zama babba ko abinda ya yi kama da haka, wannan kuma ba fa sai mabiyin nan ya tsufa ko ya dade a cikin tafiyar ake samun haka ba, ana samun irin wannan hatta a cikin wadanda basu dade ma da fahimtar al'amarin ba, musamman ya zama cewa yanzu an san shi akwai wani wuri da yake bayarda gudumuwa kuma ya yi fice a wajen, yanzu ka ga shedan yana kai masa hari da saka masa girman kai da nuna masa cewa yanzu fa shima ya isa komi sai da shi, da cewa yanzu su ne manya idan ba su ma abin ba zai yiwu ba dss.

Wato, idan Allah (T) ya yi maka baiwar fahimtar kiran Jagoranmu a wannan zamani na mu an gama maka komi, wannan bawan Allah ba karamar Rahma bane ga wannan al'ummar, sai idan mutum yana shiga cikin ita al'umma din yana fira da su zai san wannan. Ita wannan al'umma din ba ta da wani fata wanda take da yakini da shi anan gaba, ita dai kawai ga ta nan ne sakaka.

Mu, almajiran Shaikh Zakzaky (H) kamar yadda kullun muke fada cewa ba muda babban kalu bale kamar kiyaye hakkin wannan bawan Allah, da ace za mu karkatarda tunaninmu, malamanmu su yi amfani da iliminsu wajen tsaida mabiya da kiyaye hakkin wannan bawan Allah, su kuma mabiyan su kalli Jagora kawai, da yan'uwa da Allah (T) ya yi ma baiwar fahimtar wannan da'awa su kadai ma sun isa dalilin tsayuwarsu amincin wannan Kasa da Addinin Allah ya kafu daram Insha Allah.

Wajibin mabiyi ne ya taimaki wannan bawan Allah, kuma lallai taimakon nan kada ya dauka cewa idan ya yi ya yima wani ne, kansa ya yi mawa. Akwai hanyoyi na isarda hakikanin sakon nan ga yan'uwa a wannan lokacin, sau da yawa yan'uwa muna ganin cewa kamar isarda wannan sakon a cikin al'umma a yanzu shine yafi ko? Lallai tsayuwarsa a tsakanin mabiyan kafin sauran al'umma yafi muhimmanci. Idan da ace za mu tsaya manya da kanana muce akan wannan bawan Allah duk abinda aka shirya yi mana ga mu ayi mana, me muke tsammanin zai faru ga sauran al'umma?

Ita wannan Harka din tun farko duk wanda ya zo cikinta ya san abinda ya zo mawa, amma abin takaici a yanzu sai kaga karfi da yaji wani tunani na neman karkatarda tunanin mafi yawan mabiya akan kaucewa duk wata barazana, ta kai ma da za ayi waki'a a wani gari sai kaga maimakon dora alhakin wannan waki'ar da abinda ya jawo ta akan su azzaluman, sai kuma ka ga cewa yanzu ma laifin yana neman ya koma akan su yan'uwanda suke a wannan wurin, ko kuma wanda yake Jagorantar yan'uwan wannan yankin da nuna cewa su suka ja, da anyi kaza da kaza da hakan bai faru ba.

Wannan ya faru a wurare da dama, idan har zargi zai koma akan wanda aka zalunta da cewa shine ya ja aka zalunce shi, ba wanda ya yi masa zaluncin ba, dan Allah ina maganar gwagwarmaya anan? Da haka ne za a kaiga muradi? Idan azzalumi ya yarda ya baka dama ka yi Addini, idan kuma ya ki yadda ka fa sa saboda maslaharsa da ta ka, wannan shine gwagwarmayar tabbatar Addini? Su Jagoranmu basu taba cewa mabiyansu suje su zalunci wani ba, sai dai su azo ayi masu zalunci.

Ko makiyin Jagora da almajiransa ya san karya ake ace wannan bawan Allah da almajiransa za su je su mari wani ba ma duka ko abinda yafi wannan ba, ko yanzu da ake wannan shari'ar ta karya ta zalunci hatta su al'umma din sun san karya ne zalunci ne kawai, su ma azzaluman sun san karya suke. Bawan Allah da yake kokarin ya tsamarda al'umma shine kuma zai cutarda su? Shi fa zalunci yana da iyaka, idan mutum na ganin cewa wannan hanya ta su Jagora tana girma an babaro ta da yawa, ba laifi bane ya janye jikinsa lokacinda ya shirya ya kimtsa sai ya dawo abinsa a cigaba, amma ya tafi shi kadai abinsa yabar ma Jagora almajiransa, shima idan ya huta ya dawo kofa a bude take.

Ba yadda za ayi a raba wannan tafiya da fuskantar jarabawa, da kalu bale musamman daga wajen makiya. Neman sabati da kara kusanci ake yi, ba wayau da dibaru da kauce kauce ba, kyam ake so mabiya ya tsaya. Shaikh Zakzaky (H) ya yi kira, abinda ya rage ma mabiya su dake. Kuma wannan alkhairin hatta makiyan da azzaluman da munafukan duk da za su zo alkhairi ne garesu. Allah (T) ya taimaka mana, Allah (T) ka amfanar da mu.

— 18/03/2020.

Comments

Popular Posts