"MU TA JAGORANMU MUKE YI"
Ko mutuwa ko Zakzaky. Al'amarin Jagoranmu ya dame mu, shine a gabanmu. Rashin kasancewa tare da Jagoranmu a wannan lokacin shine silar haifar mana da duk halinda muke ciki, da tun tuni munce masu ko dai a saki Jagoranmu ko duk a kashe mu da yanzu an wuce wannan marhala.
Duk wanda zai iya sanya gilashi ya iya hango gazawa da laifukan Jagoranmu wannan tabbas ba mabiyi bane dan Saddu ne. Da haka wasu malamai suka so su yi da'awa a lokacin Imam Khomaini (QS), suka dinga sukar Imam da ganinsa a matsayin mai shisshigi wanda ya shiga al'amarinda ba na sa ba, almajiran Imam kuwa suka yi fatali da wancakali da su, suka rike Imam kawai, daga karshe nasara ta zo masu.
Idan kana san girmanka ya kai kololuwa kabi Shaikh Zakzaky (H), idan kuwa kana ganin yanzu kaima ka yi karatu za ka yi shisshigi za ka tsinci kanka kana ta watsal watsal. Shaikh Zakzaky (H) da da'awarsa ne mafitar wannan rayuwar, shiyasa muka ce ko Mutuwa ko Zakzaky.
Duk wanda yake jin shi dai ba zai iya bayarda jininsa ba akan lamarin Shaikh Zakzaky, to da man ba da shi muke wannan zancen na mu ba. Muna magana ne da wanda ya san cewa shi ma Jagoran nasa ya bayarda jininsa ne domin yan'cin rayukan raunanan da ake zalunta a wannan duniya.
Ko Mutuwa ko Zakzaky, wannan kam ya zama wajibi mabiyi yaji cewa zai iya bayarda Rai shima kamar yadda Jagoransa ya bayarda Rai, shiyasa ma Jagoran yace wanda duk yake ganin da man ba zai iya bayarda Ransa ba ga hanya nan ya yi gaba. Allah (T) ka yi amfani da mu wajen taimakon da'awar Shaikh Zakzaky (H), Allah (T) ka amfanar da mu.
— 11
/03/2020.

Comments
Post a Comment