Tuna tarwa ga yan uwa

Wato akwai wani abu dayake bani mmki da tsoro gameda yan uwa musamman a wannan yanayin da muke ciki, sai kaga wani dan uwa ya kawo labarin yanayin dasu Malam (H) suke ciki amma  da wuya kaga wanda zai ce uhumm akan maganar amma da zaran an kawo wata maganar ko wani wargin sai kaga anyi caa, kuma na lura kusan ko wanne group na yan uwa haka abin yake.

Babban abin tsoro ma sai kana samu kana leqawa Abuja struggle nan ne zaka qara firgita ganin qarancin adadin yan uwa da suke halarta, wato idan ka kwatanta da adadin mabiyan da akace Malam (H) yana dasu, har sai in rinka tunanin cewa ko wannan shine tantancewar da kuma tankade da rairayar dasu Malam (H) suka sha magana akai ne. Tunda duk dan uwa yasan cewa Abuja ne mafi qarfi wajen nemawa jagora yancinsa bayan addu'o'in da akeyi.

Allah ya tausaya mana kada ya musanyamu da wasunmu, ya tabbatar damu, yasa mu dawo cikin hayyacinmu, ya kuma nesantamu da fargan jaji. Bi haqqi Sayyidatul Nisa'il Alamin (as)

Share link

https://ansarulmahdi.blogspot.com/

Comments

Popular Posts