KASHE KASHEN NAN.YA ISA HAKA

KASHE-KASHEN N


Idan har babu hannun gwamnati a cikin kashe-karshen da ake yi da kona garuruwa, ya kamata ta dakatar!

Bai kamata ace gwamnati da jami'an tsaronta sun iya bude wuta ne kawai a kan Yan Shi'a masu Muzaharar kira a saki Jagoransu da ake tsare da shi bisa zalunci da danniya ba.

Almajiran Shaikh Zakzaky suna fitowa Muzaharar kira a sake shi, za ka ga motar Yan sanda da soji sun zo sun fara bude wuta da harsasai masu rai, su kashe na kashewa su raunata na raunatawa, amma yan ta'adda dauke da makamai za su je gari su yini ko su kwana suna kashe al'umma, suna kona musu gidaje da shaguna, har su gama su tafi ba wani jami'in tsaron da za ka ga ya zo da nufin fuskantarsu.

Ba ma kamar abubuwan da suke faruwa a tsakanin nan a jihar Kaduna, shi gwamnan ya iya kurin cewa ya hana mabiya Al Zakzaky Muzahara a Kaduna, don haka ma ko a makon jiya sai da ya sa aka bude musu wuta aka kashe yaro dan shekara 17, amma ya kasa hana Kashe-Kashen al'umma da kullum ake yi a garuruwan jihar. Ko a karshen makon da ya gabata yan ta'adda sun kashe mutum fiye da 50 a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Wai ta ina ma masu kashe-kashen nan ke samun makamai haka? Sun iya kera bindiga ne? Ko kuwa sayowa suke yi daga kasashen waje? Ta wace hanya bindigun ke zuwa hannunsu ne? Ta ya suke shigowa Kasar nan? Ya aka yi jami'an tsaron da aka tula a kan hanyoyi ba su iya kama su?

Comments

Popular Posts