Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya kamu da coronavirus


Gwamnan iihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ya kamu da cutar coronavirus.
Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi ranar Asabar, inda ya ce ya killace kansa.
Kazalika ya ce har yanzu bai fara nuna alamun cutar ba.
"A farkon makon nan ne na yi gwajin cutar Covid-19, kuma sakamakon ya fito a yammacin yau. Ina mai bakin cikin shaida muku cewa ina dauke da cutar," in ji El-Rufai a wani bidiyo da gwamantin Kaduna ta wallafa a Twitter.
"Kamar yadda hukumomin lafiya suka tsara kan abin da mai dauke da cutar ya kamata ya yi, na killace kaina. Mataimakin gwamna zai ci gaba da jan ragamar kwamitin musamman kan Covid-19 sannan zan ci gaba da bayar da bayanai lokaci zuwa lokaci."
Nasir El-Rufai ya yi kira ga al'ummar jihar Kaduna su ci gaba da bin dokar da gwamnatinsa ta kafa a jihar da kuma shawarwarin hukumomi domin kare kansu daga Covid-19.

Comments

Popular Posts