CORONA VIRUS (COVID-19) A NIGERIA
Wato, gaskiyar magana yaki da wannan cuta, da kuma al'amarin wannan cuta a wannan kasa akwai alamar tambaya, musamman yadda mahukunta a wannan kasa suka maida baitil malin kasar tamkar gadonsu, suka dauki talakawan kasa kamar bayinsu, suka mayarda malamai mabarata banbadawa yan korensu.
Duk mutum mai hankali ya san cewa salon yadda aka fito da yaki da wannan cuta a wannan kasa salo ne kawai na satar dukiyar al'umma, da kuma salon tsangwama da takurawa yan kasa, ta yadda za a hanasu sakat har a kaisu bango, ba tare da an taimaka masu an 'a gaza da tallafa masu ba.
Ita wannan Corona a Nigeria kamar Sallah ce tafi ki, ita tafi rashin son Sallah, musamman Sallar jam'i, masallatai a garinda nake yawancinsu duk an garkame su da kwado, abin mamaki sai kaga kuma ana Sallah a harabar, amma a cikin Masallacin an hana, ko Corona tana cikin Masallaci ne, oho. Haka nan za ace jama'a suje kasuwa su sayi abinci, amma kuma ba za suje su yi Sallah ba, yanzu fa kiran Sallah da ladanci duk babu su, sai dai kaga idan lokacin Sallah ya yi jama'a su sadada su shiga su yi sallah, ba ladanci, ba amsa kuwa.
A takaice tsarin yadda za a zaunarda mutane a gida babu shi sam sam, sannan kuma sun fito an bisu da tiyagas da bindiga. Lallai mahukuntan wannan kasa su ta ka a sannu, su sani fa zalunci na da iyaka ba fa zai dawwama ba, akwai ranar kin din lanci.
Shaikh Zakzaky (H) bawan Allah din da da'ace suna a tare damu yanzu da munji hakikanin al'amari, kuma da mun samu mafita akan Corona, ya zama wajibi masoya da mabiya mu jajirce a wannan lokacin da iya abinda muke iyawa wajen ganin su Jagora sun samu yan'cinsu, yan'cin wadannan bayin Allah na daga cikin maganin da wannan kasa za ta sha ta warke daga cutar nan Insha Allah, Allah (T) ya amfanar da mu.
—
Comments
Post a Comment