#Kalu Balen Malamai



Kalu bale ga dukkanin malamai masana arifai, musamman wadanda suke goyon baya da tausaya ga mukhlisin bawa mumini Shaikh Zakzaky (H) dan gane da zaluncin da ake masa, kalu bale ga duk wanda ya san hukuncin yin shiru a lokacin zalunci, musamman a yanzu da duniya ba ta san irin wannan zaluncin ba sai akan Muslihin bawa.

Wannan kalu bale kuwa har ga malaman da suke tare da wannan bawan Allah a fahimta guda, ko kuma a gwagwarmayance a ko ina a duniya, ya dace malamai su fito da mazlumiyyar nan su kara bitan wannan zalunci, duniya taji ta gano musabbabin fadawa cikin wannan yanayi na firgici da takunkumi.

Shaikh Zakzaky (H) malamin duniya ne ba na Africa ko Nijeriya ba, malami ne mai aiki da ya tsaya kyam akan taimakon bayyanar wanda da bayyanarsa ne komi zai dai daita. Taimakonsa taimakon Imam Mahdi (ATFS) ne, warbarda al'amarinsa kuwa warbarda al'amarin Imam Mahdi (ATFS) ne, Allah ka tsare mu, ya Allah ka kawo ma Jagoranmu agajinka da gaggawa, Allah (T) ka amfanar da mu.

Comments

Popular Posts