Lokaci Na Zuwa!
Ga alama an kusa zuwa lokacin da mutanen Kasar nan za su fito kwansu da kwarkwata su ce wa azzaluman Kasar nan tunda dukiyar kasar ba na ubanku bane! Ku sakar mana abinmu mu sayi abinci!
Muna kuma maraba da wannan lokacin, a shirye muke mu mara baya a fatattaki azzaluman da suka saukarwa da Kasar nan yunwa alhali wallahi Allah bai sanya kasar nan daga kasashe masu talauci ba. Wasu tsinannu ne yan tsiraru kawai suka rike dukiyar al'umma suke abin da suka ga dama da shi.
A lokacin da aka fito don neman abinci, za mu so yanayin ya juye zuwa ga neman yanci a kasa baki daya. Talakawa su ce sun gaji da zaluncin azzaluman nan da suke shiga rigar maceta su yi cuta. A komawa nizamin addini wanda zai shimfida adalci a doron kasa ya yalwata raunana.
Miyagun azzaluman nan ba don Allah suke garkame mutane a gida ba. Ba don basu so Talakawa su mutu bane, wallahi karya ne, kawai suna yi ne don cutar kar ta shafe su, da ace ko Talaka ya wataya su za su tsira daga cutar nan da in ana kara ma mutane cinkoso ma za su yi.
Kun ga dai yadda suke bin mutane da Tiyagas (a wani video da ake cewa Kaduna in ya inganta) akan su shiga gida a kulle su, wanda duk ya tunkare ka yana harba maka Barkonun tsohuwa wallahi ya yi karya idan yace maka wai yana hakan ne don yana so ka tsira da rayuwarka daga wata cuta. In har haka ne ba zai yiwu ya saka maka hayakin da shi kansa cuta ne kuma ma yana kisa ba.
Zaluncin azzaluman kasar nan ya yi yawa. A Kasar nan akwai dukiyar da in duk dan Nijeriya za a bashi kyautar Naira dubu dari biyar (500,000) a daidai wannan lokacin, wallahi ba za a girgiza ba. Amma sai dan banza siyasa da yaudara ake ma mutane kawai, ana kuntata musu, ana hana su hada-hada da harkoki tare da cewa kashi 90% dinsu sai sun fita suke neman abin da za su ci. Ba a basu ba an hana su su nema, kuma ana cutar da su da dukkan kuntatawa.
Allah Ya sa cutar nan ta hallaka duk azzaluman nan da ke wadaka da dukiyar al'ummar kasa, da masu takura musu. In Allah Ya hukunta ta shafi wanda ba shi da hakki, Allah Ka karbe shi a matsayin Shahidi.
Comments
Post a Comment