COVID-19: Tabbas Miyagun Mutane Ke Mulkin Kasar Nan



Na ji matukar takaici da na ga wannan rumfar mai kama da rumfar Injin yankan Katako. Ko kunya Gwamnatin Kano bata ji ba tana yada hotunan a matsayin wani bajinta da take yi wai tare da hadin guiwar Dangote wai a kokarin yaki da CoronaVirus.

Yanzu wai wannan rumfar ita ce ake sa ran za a tattara akalla mutum 600 na masu cutar CoronaVirus idan sun kamu nan gaba a jihar Kano. Sai kace wasu 'yan gudun Hijira.

Ya Allah Ka tsinewa azzaluman mahukuntan kasar nan. Ka debe musu albarka. Ka tattara duk jifa'i da bala'in annobar nan a kansu.

'Yan iska kawai matsiyata. Kawai saboda duniya ku yi ta wasa da rayukan mutane? Yanzu in cutar ta kama mutane a wannan runfar za a tattara kowa da kowa kamar yan gudun hijira kenan har su karisa?

Ana gina wuraren baiwa al'umma kariya a inda suka san ciwon kansu, ku kuna buga rumfa da katakwaye a sararin samaniyar Allah? Wane irin zalunci ne da mutanen nan haka? Tir!

Sai yawo ake da lambobin kudaden da za su yayewa duk yan Nijeriya Talauci, amma a tsakanin wasu tsirarun barayi mayaudara makaryata, ana ta gara Talaka?

Don Allah ba abin kunya bane a nunawa duniya cewa wannan rumfar ce mai kudi irin Dangote da Gwamnan jiha guda suka hada karfi suka samar wai don killace masu cutar Corona ba?

Wannan ya nuna cewa in cutar nan ta yi kamari a kasar nan kawai za a rika karisa mutane ne a filayen kwallo da dazukan bayan gari.

Wallahi miyagun azzalumai ne na gaske ke rike da kasar nan. Sun cika azzalumai sosai.

Allah Ka tsine musu albarka. Ka sa su ci bala'in da zai cinye su a wannan Karon.

Comments

Popular Posts