Dauri A Makyankyasar Kwayoyin Cuta
Daga Ibraheem Zakzaky
Duniya ta tsinci kanta a cikin wani irin hali na bullar annobar Coronavirus; cutar da ta haifar da matsanancin tsoro da birkita lamurra. Wannan annobar ta zo da wani salo da ya saba da sauran cututtuka masu yaduwa, tana yaduwa ba tare da bambancewa ko la’akari da bin mugun tsari irin wanda aka yi amfani da shi wurin tsara kisa da batar da wasu ba, ciki kuwa har da ‘yan uwana shida. Gaggawa cutar take yi a lokacin da ta fara mararin kashe wadanda ta rubuta kashewa. Fiye ma da gaggawa irin ta Buhari.
Annobar Cutar ta fi kama da irin annobar da za a yi fama da ita a karshen sa’i. Hatta wadanda suke da kololuwa a taka-tsantsan sun tsinci kansu a yanayi na rashin sanin takaimaimen yanayin wannan cuta da yadda za a fuskance ta. Ko da yake da yawan masana a fannin kiwon lafiya sun dukufa wurin nemo rigakafin wannan cuta kafin nan da wasu watanni masu zuwa ko shekara ma; zancen gaskiya dai, wannan hatsari ne da ba a san kololuwarsa ba.
A fannina, ina rayuwa ne da zimmar kullum gari ya waye na kai wa iyayen abinci da magunguna a Kurkukun Kaduna; wanda kwatsam! Sai aka wayi gari abubuwa na neman dagulewa. Ina sane cewa, gabadaya gwamnatin nan ta Manjo Janar Buhari ce ke fuskanta wannan muguwar annoba ta Coronavirus.
Sai ya zama an haramta duk wata irin ziyara zuwa Kurkukun. Na iya fahimtar cewa, wannan mataki ne da aka dauka domin a hana bullar wannan muguwar cuta a Kurkukun. Wanda kuwa ba zan so a ce wani aiki nawa zai taimaka wurin zafafa rashin lafiyar iyayena ba.
Na kammala duk wani shiri na likitocin da za su je Kurkukun Kaduna domin duba lafiyar mahaifana da ke ci gaba da tabarbarewa, sannan ga kuma raunukan harsasai da suke dauke da su sakamakon farmakin da sojoji suka kai a gidanmu. Duk raunuka da cututtukan da suke fama da su an ki yi musu magani na tsawon shekaru biyar kenan.
Duk da haka ina da ra’ayin a killace wannan wurin a matsayin matakin kiyayewa na dan gajeren lokaci, kafin a ga yadda yanayi zai bada. Saboda wannan ne ma na nemi afuwan dukkanin likitoci da asibitocin da na nemi su duba mahaifana, domin a bi ka’idar killace kurkukun na Kaduna. Na yi kokari iyaka iyawata wurin aikawa da abin rufe fuska, safar hannu, sabulai da magungunan gina garkuwar jiki. Duk dai don ya zama kowa na cikin aminci.
Sai dai fa yanzu hankalina a tashe yake da labarin da na samu. An samu afkuwar wani yanayi a Kurkukun na Kaduna, wanda ya sa na tuna da kisan kiyashin da aka aikata a Zariya a shekarar 2015. Yayin da aka yi ta jiyo karar harbin bindiga daga Kurkukun Kaduna, inda a nan ne iyayena suke tsare.
Duk kokarin da na yi na son samun Kwanturola din Kurkukun da mataimakinsa a yawa abin ya ci tura don ba su dauki wayata ba, yayin kuma da aka ci gaba da harbe-harbe a ciki. Duk wani kokari da na yi na son sanin hakikanin abin da ke faruwa a ciki shi ma ya ci tura. Sai dai na iya fahimtar wasu ‘yan abubuwa daga wayoyin da na yi. Gabadaya sun tafi akan cewa:
1. An samu ‘yan fursuna masu dauke da cutar Coronavirus a Kurkukun Kaduna
2. Ma’aikatan lafiya na kurkukun sun yi ta kauracewa wasu ‘yan fursuna uku da ke dauke da cutar.
3. An fitar da su ukun, inda kuma a ranar Talata aka dawo daa mutum daya.
4. Wsu daga cikin ‘yan Fursunan sun yi bore kan dawo da wannan fursuna mai dauke da cutar.
5. Jami’an gidan yarin sun yi kokarin kwantar musu da hankali, ta hanyar lallashi.
6. An kawo rundunar musamman da ke kula da Kurkukun domin su dakile zargin ballewa daga Kurkukun.
7. Bayan an dauki lokaci ana harbe-harbe an iya natsar da lamurra a Kurkukun.
8. Daga cikin ‘yan fursunan da ake zargin suna da cutar Coronavirus suna cikin wadanda aka kashe a harbe-harben.
9. Har zuwa awa uku bayan abin akwai fankon harsasai a farfajiyar Kurkukun.
10. Many of the Kaduna prison staff are visibly injured, some with serious injuries.
11. An iya ganin wasu daga cikin jami’an Kurkukun da aka raunata a lamarin suna yawo da khaki a jikinsu, ga kuma jini na zuba.
12. An ce wai an daidaita komi, wanda Allah kadai ya san irin barnar da aka yi.
Maganar gaskiya ita ce, wannan muhallin na Kurkukun Kaduna wanda ke fama da cinkoso da rashin tsafta, ba wuri ba ne da ya kamata a ajiye iyayena wadanda dukkaninsu sun haura shekra 50. Kuma dukkaninsu suna fama da rashin lafiya, kowannensu na da wata cuta wacce aka ki a dau matakin kula da ita.
Ganin irin zakuwa da wannan gwamnati ta yi, gwamnatin Manjo Janar Buhari da mugun gwamna El-Rufai da makasan sojojinsu. Bani da tabbaci kan hakikanin abin da ya faru bayan harbe-harben da aka ji a Kurkukun Kaduna. Baya ga wadancan abubuwan da na zayyana a sama, ban san komi ba.
Daga Ibraheem Zakzaky
Comments
Post a Comment