TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY DAGA BAKINSA (2)
A lokacin da nake jami’a akwai wani yanayi da na samu, wanda kuma shi ya taimaka wajen canza rayuwata. Lokacin da na shiga (jami’a) kamar kowane dalibi, fatata shine na kammala jami’a wala’alla na je na kama aiki, ko kuma ma na cigaba da karatu a nan jami’a din, to amma yanayin da muka samu kanmu a ciki a wannan lokacin na karshen 70s, kamar za a iya cewa akwai musayar ra’ayi dangane da abin da ya dace ya zama makomar kasa.
Lokacin kwaminisanci na tashe sosai, kuma da yawan dalibai da suke nuna sun waye, Kwaminisanci suke yi. Haka suma cikin Lakcarori wadanda suke nuna su cigababbu ne to Kwaminisanci suke. Saboda haka Kwaminisanci kamar shine wata alama ta cigaba.
Kuma Kwaminisanci na da matsalar cewa suna ganin addini kamar wani mummunan abu ne. Kuma su kan ta yin hujumi a kan addini baki daya, da kuma musamman ma Muslunci. Suna ta sukan Musulunci, suna nuna kamar irin sarautan gargajiya da kuma mulkin Banu Umayya, Banul Abbas da Usmaniyawa duk sune ma’anar addini.
To, da yake ni ina da asasin addini, duk da yake shi wannan karatu (na boko) na shige shi ne, amma asalina na karatun addini ya fi karfi. Saboda haka ni ban jahilci addini ba. Don haka sai ya zama muna shirya lakcoci muna maida musu da raddi akan mene ne hakikanin addinin Musulunci.
Na’am, an yi mulkin Banu wane da Banu wane da sarautan gargajiya, amma sarauta baya wakiltan addini ko da an yi shi da sunan addini. Kuma abin da sarakai suke yi ba laifin addini bane. Kuma in ana zalunci, bamu ce ba a zalunci ba, amma ba sunanshi adini bane. Shi addini daban ne, kuma abin da mutane suke aikatawa daban. Ba yadda za a yi mutum musulmi ya aikata aiki, sai ka hukumta Musulunci da aikinsa. Ko sauran mutane in muka musu irin wannan hukuncin, hatta su ‘yan Kwaminis din, in muka hukunta su da abin da ‘yan kwaminis suke aikatawa suma ba za su yarda shine Kwaminisanci ba. Sannan kuma muna nuna cewa shi abin da duk suke bukata wajen kawo sauyi, shi addini yana da shi.
Don haka a wannan lokacin, muna iya cewa kamar mun kasu kashi uku; Akwai masu ganin makomar kasa Musulunci ne. akwai masu ganin nizamin da yake zaune a yanzu ya musu, kamar Kiristoci. Akwai kuma masu ganin cewa Kwaminisanci ne za a yi. To, kaga wannan ja’inja din shine za mu iya cewa asalin dagowar gwagarmayarmu.
To, a lokacin kuma muna cikin haka nan ne, aka samu juyin-juya hali na Iran, da bayyanar Imam Khumaini (QS) a karshen 70s din, wanda kuma sai ya bamu fata, ya zama cewa abin da muke fatan zai auku, wanda su suna ga ba ma zai yiwu ba, to zai iya aukuwa a wannan zamanin.
Saboda haka bayyanar Imam Khumaini da kuma juyin Musulunci na Iran ya yi tasiri a kanmu sosai a karshen saba’inoni, tun lokacin Imam Khumaini yana Daransa, kafin ya koma Iran. Wanda komawarsa ne ya ba da tabbatan wannan nasarar. Karshen saba’inoni lokacin ina iya cewa ina shekarar karshe kenan a Jami’a, don a 1979 na fita.
To, wannan gwagwagwa din tsakaninmu a jami’a, sai su hukuma suke ganinshi a matsayin hadari. Sai suke ganin mutum kamar ni da wasu ire-irena bai kamata ma a kyale su su kammala jami’a su dawo cikin al’umma ba, domin za su iya canza su. Saboda haka suna da wata manufa ta daban (a kanmu). Wadansunmu daga wadanda aka ce an kore su, an basu takardar (kora) kai tsaye, sai wadanda aka ce su maimaita shekaru, bayan mun san suna da hazaka. Sai kuma irin su n, wand aba a a ce an kore ni ba kai tsaye, amma ba a bani ‘certificate’ din gama karatun ba. To, wannan sai ya za na koma ma aikin addini din kawai.
Farkon 1980 kuma sai ya zama na halarci bikin farko na nasarar juyin Musulunci na Iran. Dawowana daga Iran a 1980 din nan, kusan ya zama wani abu ne kamar bakon abu. Don a jami’ar ma lakcan da na yi (a ABU) wasu takawa suka rika yi da kafa kilomita biyar zuwa bakwai, suka zo don su ga wanda ya je Iran kuma su saurare shi. Saboda haka yay i tasiri sosai.
Kuma ba a ABU kawai nayi magana ba. Na yi irin wannan shigen maganar (na tsarabar zuwa Iran) a jami’o’in kasar nan da yawa. Kamar misali jami’ar Lagos, a nan ma na fara jawabi, da Ibadan, da kuma Jami’ar Ilorin, jami’ar Jos, da Jami’ar Maiduguri, da jami’ar Bayero da ke Kano da kuma jami’ar Sokoto, a lokacin ba a saka mata suna Usman Dan Fodiyo ba. Da wasu wurare ma, duk na je na ba da lakcoci akan abin da idanuna suka gani tafiyata Iran. Kuma yay i tasiri sosai.
Za mu cigaba.
© www.cibiyarwallafa.org
Comments
Post a Comment