WANI BURIN JAGORA (H)
“Wata kila za mu so mu ga cewa muna da wadansu jiga-jigai kamar mutum 70, kowanne a cikin 70 din nan, yana iya Jagorancin mutum miliyan goma. Wato, Miliyan goma din nan za su iya dogara da shi, kuma shi zai iya basu fatawa kan kowace mas’ala ta addini, muna iya ce masa dai Jagora a takaice.
“To, kuma karkashin 70 din nan, ya zama akwai wadansu wadanda suma jiga-jigai ne, amma ba su kai 70 din farko ba, amma su kasance kamar su 700, ya zama kowannensu ka bashi wata kila mutum miliyan daya, to shima zai iya Jagorantarsu.
“Sannan a karkashin 700 din nan a samu wasu kamar su kumu dubu bakwai (7,000). Kama-kama dai har ta kaima ko da kauye ne, kuma komai kankantar kauyen, ya zama akwai wani mutum ne zaunanne wanda shi zai iya ma jama’a tarbiya.
“In da za mu samu haka nan, da shikenan, su mun san mutanen gari nasu sassauka ne, basu bukatar dole su zama Malamai, dama ‘mustahili’ ne kowa ya zama Malami. Dama a addinin nan ba a ce kowa sai ya zama Malami ba. Su suna bukatar su amincewa Malam ne kawai, Malam yace ai kaza domin haka yake a addini, su kuma su yi, Malam yace a bar kaza, sai su bari. Su suna bukatar ne kawai a nuna ga inda za a je, sai kawai su kama hanya.
“Amma in ya zama muka kama abu duuu, muka zama kamar ja-jama’a, ya zama kawai mutane sun bumbunto duuu, alhali ba irin wadannan jiga-jigan da muke zance, to zai zama za a yi abin da Hausawa sukan cema ‘runguma ni mu fadi’.
“Wato kenan zai zama in su mutane suka zo duuu, alhali ba a shirya basu Jagoranci da tarbiya wadda ta kamata ba, kuma basu ganin alamin addini a wajen masu jawo su din, to karshen al’amarin su za su ja abin ta yadda suke ganin ya dace. Kuma idan su suka ja abin, zai zama in kaga Harkar abin da su suke yi ne za ka gani.
“Don haka yana da muhimmanci, ya zama in ana da’awar nan ya zama ana dauki dai-dai. Daukar dai-dai na da muhimmanci, ta yadda za ka samu da’irar ‘yan uwa ‘kalilan’, kamar nace akwai ‘yan uwa goma sha bakwai (17) a da’irar, misali. Wadannan yan uwa 17 din suna da Da’ira, suna da Qa’id (Jagora) a cikinsu, wanda ke basu darussa, kuma in abin ka zo ka samu 17 din nan ne, za ka same su ginannu ne a kan wata dabi’a ginanna. Suna da wata al’ada ginanna. Sun siffata a ayyukansu da zantukansu da siffarsu (wanda ido ke iya gani) da addinin nan. Ta yadda in mutum na 18 ya zo ya samu 17 din nan a wannan ginin, to yana da sauki gare shi nan da nan ya zama irinsu. Haka kuma idan ya zama bayan na 18 aka samu na 19 ya zo, shima ya samu 18 din nan ginannu ne a kan wani abu, sai a tafi tare. Haka nan na 20, da sauransu.
“Har ta kai ma in dai da irin wannan dauki dai-dai din ne har aka yawaita, to ‘falillahil-hamd.’
“Amma idan ya zama kamar akwai da’irar ‘yan uwa kamar mutum 17 ginannu a kan wannan Harkar, sai wata rana mutum 170 suka zo suka shiga ciki, su kuma 170 din nan basu da tarbiya a kan abin da mutum 17 din nan suka ginu a kai, me kake tsammanin zai faru? In ka hada 170 din nan da 17 ka samu mutum 187 kenan ko? Me za ka gani a wajen? ‘Dabi’ar 170 din nan za ka rika gani. Don su 17 din nan sun zama ‘yan tsiraru, ba ma za a iya ganin dabi’ar su ba. In ka zo abin da wadannan 17 din suke gine a kai ba shi za ka gani ba, wanda mutum 170 din nan suka shigo da shi, shine za ka gani.
“Ta yadda kenan in har aka kyale irin wannan misali ya auku, zai zama kenan kila ma an fizgi su 17 din, in kuma ba a fizge su ba shikenan sai a rabu biyu. Wannan yai nan, wannan yai can.”
- Bangaren jawabin Jagora, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a wajen wani ‘Ijtima’ a shekarun 1990s, jawabin da aka ma take da ‘Mu ba kungiya bace’. Saifullahi M. Kabir ya rubuto daga ‘audio’ din.
Comments
Post a Comment