#Duniya ta yi Shiru



Tambaya, me yasa duniya ta yi shiru akan wannan zaluncin da aka ma mukhlisin bawa muslih mumini? Bawan da yake son kawo gyara a cikin al'umma. Me yasa duniya ta yi shiru, ba ta yi abinda ya dace ba, al'ummar musulmi ba su yi abinda ya dace ba, kasashe da suke da ikon yin abinda ya dace su ma ba su yi abinda ya dace ba, masoya da mabiya da masu goyon baya su ma sun takaita sun gaza yin abinda ya dace, me yasa?

Yin shiru da rashin tabuka abinda ya dace akan bawan Allah Mazlumin wannan karni, wanda yake ta sa'ayin ganin ya aikata aikin da cikar aikin zai bayyanar da Shugaban da zai zo ya taimaki wannan duniya daga fadawa da ta yi cikin tarkon wahala, da tsamar da ita zuwa yan'cin walwala da adalci, Al Imam Mahdi (ATFS). Rashin taimakon wannan bawan Allah zai iya jawo ma duniya fadawa cikin halin kaka nika yi, da tsunduma cikin takun kumin da Allah (T) kadai ya san ranar fita.

Matukar wannan duniya ba ta dawo cikin hayyacinta ba, tabbas al'amarin hakkin wannan bawan Allah zai iya kawo ma wannan duniya cikas.  Taimakawa wannan bawan Allah na daga cikin abinda Allah (T) zai dubi wannan al'umma ya kawo mata a gaji, rashin taimaka masa kuwa zai kara janyo ma duniya musiba da bala'i ne. Allah (T) ka sa mu a cikin masu taimakon wannan bawan Allah, ka yi amfani da mu, Allah (T) ka amfanar da mu.


Comments

Popular Posts