TARIHIN SHAIKH ZAKZAKY DAGA BAKINSA (1)
— Daga Littafin Harkar Musulunci na Cibiyar Wallafa
Bismillahir Rahmanir Raheem.
Sunana Ibraheem Zakzaky. An haife ni ne a Zariya an shekara ta 1953 Miladi, wanda yayi daidai da Hijiri Kamari 1372.
Mahaifina Malamin Alkur’ani ne, haka ma kakana, shima Malamin Alkur’ani ne, haka ma shima uban kakana. Sai dai shi uban kakana da kuma kakan nawa a lokaci guda suna karantar da karatun littafi irin su Fiqihu da ire-irensu baya ga karatun Alkur’ani. Amma duk cikarsu mahaddata ne, kuma kwararru a kan Alkur’ani din. Kuma har wala yau su kan hada da yin noma a matsayin hanyar rayuwa, baya ga koyar da karatun Alkur’anin.
To, haka nan kuma ita ma mahaifiyata, bangaren gidansu suma Malamai din ne. Da yake tsarin rayuwa a wajenmu a da, kusan kowane abu iyali ke yi. Wato akwai wadanda suke sarakai ne, akwai wadanda suke Malamai ne, akwai wadanda kuma ‘yan kasuwa ne. To, ni ta bangaren uwa da ubana duka abin da ya shafi Malinta suke yi.
Na’am, akwai dangantaka da su sarakai din, don iyayenmu su suka rika koyar da nasu iyayen. Kuma tafiyar (rayuwar) kamar tare ake yi, sai dai kowa da abin da yake yi, za ka ga mutane basu cika dauka sarauta suke yi irin na gargajiya kafin zuwan Bature ba.
Asalin iyayenmu sun fito ne daga Magrib, Maroko kenan na wancan lokacin. Musamman ma daga wani birni da ake ce masa Shingidi, wanda yanzu yana cikin Murtaniya ne. Amma a lokacin babu Murtania, Shingidi ake ce masa. Kuma sun tashi daga sassa zuwa sassa har suka zauna a Mali ta da. Kuma daga can suka zo nan. Ana cewa suna daga cikin ‘sulala’ din Imam Hasan Almujtaba (AS) wadanda suka zauna a kasar Magrib. Daga nan suka gangaro sukai Mali, suka fado nan kasar.
Bayan tasowa ta dai na fara karatu a wajen mahaifina ne. Kamar yadda n ace shi Malamin Alkur’ani ne. Kuma Alkur’anin na karanta a wajenshi. Abin da muke ce ma babbaqu (haruffa kenan), da farfaru (shine a daura musu wasulla), sannan kuma da tashiya (wato mikewar karatu).
Sannan kuma duk da haka ya saka ni a wani makarantar Alkur’ani na wani Malami daban, wanda yake akwai yara da yawan gaske da suke hadda a wajen. Sannan kuma a lokaci guda muna yin wannan karatun kuma muna taimaka masa a aikin gona.
Muna da wani ka’ida na cewa sai ka sauke Alkur’ani za ka fara karatun littafai (na azure). Saboda haka bayan na sauke din sai na fara karatun littafi, tun kamar ina dan shekara 14. Karatun littafai wanda dai ake yi a nan kasar daidai gwargado na yi su. Ta fuskacin Lugga da Nahawu da Sarfu lallai Nijeriya bata gaza sauran sassan duniya kamar Misira da Iran da Iraq ba, duk kusan littafai daya muke karantawa. Kuma daidai gwargwado na karanta tun daga kananan littafai irin su Ajruma, Mulha, Saja’I, Alfiyan Dan Maliki. Duk mun yi wadannan. Sannan kuma ta bangaren Lugga akwai mu da littafan da mu a nan ake karantawa a Afirka ta yamma, galiba na yabon Manzon Allah (S). Irinsu Ishiriniya, da Witriya da Ashariya, kuma daga nan akan je ga wasu littafai da aka sani a waje, sune Makamatul Hariri, da kuma Shu’ara’ul Jahilyya.
To, ta bangaren Fiqihu, Fiqihun Malikiyya ne dama ake yi. Shima kuma daidai gwargado duk littafan da ake karantawa a karatun Fiqihun Malikiyya, shima na karanta har ya zuwa littafin da ake ce ma Muktasar. Wanda wannan littafin har ana masa kirarin ‘abokin samartakan yaro, abokin kuma tsufan tsoho.’ To, daidai gwargado mun yi yarintaka da shi, mun kuma manyantaka da shi.
To, haka kuma dai wannan karatun gida, ina cikin yi kuma na shiga Nizami a shekara ta 1969, lokacin ina kamar dan shekara 16 kenan. A lokacin zan iya cewa na fara karatun da za a ce masa ‘Nizami’, wato tsararren karatu. Wanda shi wannan wata makaranta ce da ake koyar da dalibai wadanda suke da asasin karatun gida, wasu ma sukai Firamare irin na makarantun zamani. Ita makarantar ta wuce Firamare, amma bata kai Sakandire ba. A nan na fara.
Shi kuma karatun da ake yi na Arabiyya ne, amma a tsare (Nizami). Saboda haka shi karatun bai kai tsaurin na gida ba. Don zan iya tunawa da muka je can akwai wani littafi da ake ce mishi Durusun-Nahawiyya, wanda mu wanda muke karantawa a gida sun fi wannan wahala. Saboda haka nag a Nahawu da Lugga suna da sauki a nan a kan wanda na karanta a gida.
To, sannan daga nan kuma sai na tafi makarantar da ake cema ta koyon Larabci (Madarasatul Ulumul Arabiyya) a Kano, daga 1971-1975. To, shima nan ana koyar da dalibai ne domin su zama Malaman makarantu. Ana sa ran za su koma su koyar a Firamare a matsayin Malamai.
A nan ne kuma a sha’awar kashin kaina na karanta wasu fannoni da ba a karantawa a nan. To, akwai kuma wani lokacin da muka yi bangaren ingilishi da duk fannonin da aka sani ana karantawa a manyan makarantu.
A lokacin da nake wannan karatu na Madarasatu Ulumul Arabiyya a Kano, to na zama ina da sha’awar karanta wasu fannoni da ba a karantawa a Makarantar, wanda ya hada da English Literature wanda na yi don kashin kaina, da Economics da Government da ma Luggar Hausa wanda shim aba a karantawa, da Arabiyya da Islamic Studies a Advance Level. Amma akwai azuzuwan yamma da ake yi domin wadannan. Saboda haka sai na halarci azuzuwan yamma din.
To, kuma bayan kammala wannan makarantar na zana jarabawar fita makarantar. Kuma bayan nan da ‘yan watanni, sai na zauna jarabawar da ake ce ma ‘advance level’, shima a kan fannoni hudu; Hausa, Islamic Studies, Economics da Government. To kusan jarabawowin guda biyu sun fito lokaci guda ne. da jarabawar da ake ce ma Grade Two Certificate a Lokacin, da kuma na shi Advance Level din.
Fitowansu a 1976 sai ya bani damar fara karatun jami’a kai tsaye ba tare da nay i sharan fage ba. Wato, na fara Degree Course a Jami’a a kan Ecnomics, Government da Sociology, wato fanni uku. Wanda daga baya na kware a Economics, na kammala a shekarar 1979. Saboda haka duka-duka karatuna na Nizami daga 1969 ne zuwa 1979, kamar shekara goma kenan.
Za mu cigaba.
© Www.cibiyarwallafa.org
Comments
Post a Comment