Skip to main content

#Coronavirus: 'Yan Shi'a Za Su Yi Wa Masallatan Kano Feshin Magani




Mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky sun kammala shirye-shiryensu domin yiwa masallatan garin Kano feshin magani a wani yunkuri na tallafawa wajen dakile yaduwar cutar Koronabairos a Nijeriya.

Da yake shaidawa manema labarai matakin na su, Dr. Dauda Nalado ya yi bayanin cewa Harkar Musuluncin tuni ta fara ayyukan wayar da kan al’umma akan muhimmancin kare kai da matakan bi wajen kare kai daga cutar Koronabairos tare da bin shawarwarin ma’aikatan lafiya wajen wanke hannu a kai-a kai da sauran su.

Comments

Popular Posts