#NAJERIYA, ASALINTA DA MA’ANARTA



“Da farko ita Nakeriya din kanta, Najeriya kasa ce da Turawan mulkin mallaka na Inglishi suka kirkiro. Ba su suka yi kasar ba, wacce muke takawa, da koguna da tsire-tsire da sauransu, Allah ne ya yi wannan. Kuma ba su suka yi mutanen kasar ba, dama can akwai mutane. Amma kan iyaka da aka zana din nan, to sune suka kaga wannan, abin da ake nufi da su suka kirkiro nenan, kuma suka ba wannan iyaka suna. Wannan kuma sun yi ne a yayin da suka fara da ribibi na Afrika, abin da suka kira ‘Scramble’ watau suka hada da al’ummominsu daban-daban na Turai, wadanda suka hada da Fransawa, Jamusawa, Focugalawa da Birtaniyawa da sauransu, suka bazu a sassa daban-daban na duniya domin bunkasa da fadada daulolinsu a wajen duniya. Abin da ya ingiza su ga yin haka shi ne akidan ‘yan kasanci, da jin cewa kowacce daga cikinsu ita ta fi dacewa da kowacce duniya, kuma suna kokarin su ga cewa sun mamaye duniya sun kafa daular da ta fi kowacce. Har wala yau da yunkurin ya zama cewa ko tq halin kaka sun kwaso arzikin wuraren da suke zuwa la’alla arziki ne da Allah yw binne a kasa, ko arziki ne na su mutanen wurin, ko ma su yi amfani da kwakwalen mutanen, domin su tattara su je su bunkasa al’ummarsu ta gida”.

“Saboda haka ko da Turawa suka taho nan, Ingilishinsu ne da Faransawansu ne, da Jamusawansu ne da Focugalawansu ne, da Italiyawansu da sauransu ba su zo domin mu ba, sun zo domin kashin kansi ne. Ba su zo domin wani abin da zai amfane mu ba, a’a sun zo ne domin abin da zai amfane su. Sun zo ne neman dukiya mai yawa musamman na danyun abubuwa da za su iya sarrafawa a masana’antunsu, da kuma diban ma’aikata masu arha, wadanda suka maishe su bayi. Da nufin kuma su samu wasu wurare da za su tsugunar da wasu masana’antunsu ta yadda za su yi amfani da ma’aikata masu arha tamkar bayi domin bunkasa kasarsu. Don haka Ingilishi ko kusa bai zo kasar nan don mitanen kasar nan ba. Bilhasali ma abin da ya kawo su ya bayyana a irin sunannakin da suka ba wuraren da suka zo. AlaliAlalisali lokacin da suka zo nam ta ruwa tekun Atlantika sun fara hulda da mitanen gefen ruwa, inda tekun Legas take a yanzu. Ba su yi wata-wata ba sai suka kira wurin da sunan abin da suke samu a wurin, suka ce gaban bayi, ‘Slave Coast’ kila da ba don sunan ya cika bakin jini ba, to da maimakon Nijeriyw da sunanmu ‘Slave Cast’. Domin ‘Ivory Coast’ ba ta gushe ba tana amsa sunan ‘Ivory Coast’. Ma’ana gabar hauren giwa, domin a nan suke zuwa su sayi hauren giwa. Har yanzu suna kasar ma kenan ‘Ivory Coast’ ko kuma Kudebuwa da harshen Faransanci. Larabawa ma suma fassarawa da suna cewa sahibul Arj wato gaban hauren giwa”.

“Kazalika inda suke diban zinare a wajen gaban da ake kira yanzu Ghana, ita ma an kira ta da wannan sunan “Gold Coast’, wato gaban zinare, dominba a nan suke diban zinariya. Ko da ganin sunayen da suka ba wuraren, sun ba sunayen albarkatun da suke diba ne, can suna diban hauren giwa, suka kirashi da gaban hauren giwa; can suna dibar zinariya, suka ce gaban zinariya, nan suna diban bayi, suka ce gaban bayi. Ko mashigiza a ce masa? Har wala yau sunan da suka ba mu a baya ya nuna irin yadda suke kallon mu, domin lokacin da suka zo suna neman hanyar da za su bi su shiga cikin wadannan wurare ta tudu, ta yin amfani da koguna da suka keta ta wurin, suna da labarin kogin Neja, amma ba su san cewa, ko yana iya biyuwa ba. Shi kogin nan da aka ce ma Neja, su suka bashi, domin mutanenmu suna da sunannaki daban-daban da suke kiransa. A wajensu nan muna ce masa Kwara. Daga jin sunan ma harshenmu ne. Irin ruwa da ya gudana da karfi akan ce ya kwarara, a nan garin ma akwai makwarari. Ka ga Kwara na nufin kwarara kenan. Amma su da suka zo sai kira shi da wani suna. Domin su suna kiranmkiranmu mu bakake da wani irin suna na wulakanci, “Nigga”. A Amurka wannan suna na ‘Nigga’. Na wulakanci ne. Ita wannan kalma ta “Nigga” ita ce dai Bafaranshe yake cewa “Nijar”. Daga nan ne fa shi kuma Ingilishi sai ya ce ”Naija” kogin bakin fata, bakin kuma na wulakanci, mara hankali. Saboda haka ko da a kira wannan kogi, kogin Neja, ana nufin kogin baki mara hankali. Sai aka samu kasa wacce daga baya aka rada mata wannan sunan, Najeriya, kasar bakake marasa hankali. Domin ba baki ne kawai ba, har da wulakanci a wannan kalma ta “Nigga”. Da can lokacin da suka kama Legas sun sa mata suna koloni na Legas. Sannan a yayin da suka yi ta kokarin kakkama inda duk za s kama, tsakaninsu da Faransawa da Jamusawa da sauransu kowannensu sun yi kokarin su kafa hulda ne da wadannan wurare domin su ce wannan yankin nasu ne. Don haka Ingilishi da Faransawa da Jamusawa suna ta ribibi, kowa na ta kokarin ya ga ya riga wani zuwa. Akwai wani baturen da ya yi ta kokarin ya ga yw je Borgu, da zuwa sai ya samu har Faransawa sun zo har sun sa Sarkin Borgu ya dora hannu a takardarsu... ”.

—Shaikh Ibrahim Zakzaky (H), cikin littafin Najeriya Ina Mafita?

Comments

Popular Posts