jaddada Bara'a
Ahmad Abdullahi Assaminaky
Wannan lokaci, lokacin jaddada bara'a ne, lokaci ne na kara kwakkwafa tunani akan alkawarinda muka dauka na cewa komin wuya da tsanani za mu kasance tare da Jagoranmu, ko da kuwa za a daka mu a turmi ayi kuli kulin kubura da mu.
Lokaci ne na tantancewa, lokaci ne da mabiyi da kansa yake iya tantance kansa, ya gane a ina wila'arsa take? Lokaci ne da ya kamata mu kara kaimi mu jajirce mu dake, lokaci ne da ya kamata mu faranta ran wannan bawan Allah da dakewarmu da juriyarmu kamar yadda suka tsaya kyam har abinda ya same su ya same su.
Jaddada bara'armu a wannan lokacin tafi kowane lokaci muhimmanci, a lokacin tsanani ake tantancewa ake gane wanene ba wanene ba, mu yi azama mu kara kaimi kuma mu roki sabati kada a tankade mu, Allah (T) muna rokonsa ya Allah kar a barmu da dibarar mu, a sa mana hannu mu kai labari
Wannan lokaci da muke ciki, lokacin daga sauti da murya ne da fito na fito da zaluncin azzalumai, lokaci ne da ba ya bukatar wata murya da za ta dankwafarda mabiya akan al'amarin yi ma zalunci tawaye, lokaci ne da ya kamata a samu irshadi na yi ma Jagora bai'ar ko a mutu ko ayi Rai, lokaci ya wuce da za yi sadda sadda da sando da rara gefe, lokacin aiki ne, sakamakon yana wurin Allah (T), Allah (T) mai karbar tuba ne daga wajen bayinsa, idan muka ce mun tuba muka gyara sai muga taimako cikin lokaci, Allah (T) ya karbi tubarmu ya yafe mana, Allah (T) ya amfanar da mu.

Comments
Post a Comment