Sabon salon yaudara:
Wasu yan damfara sun fara kiran mutane suna cewa za a basu kyautar kudi Naira 20,000 ko kasa da haka ko sama da haka daga Gwamnatin Tarayya (FGN), sai su nemi ka turo BVN Number din Bankinka.
Ka kiyaye, karya suke yi. Kar ka yarda ka tura musu BVN ko wani bayani akan Bakinka, za su damfare ka ne su sace kudin asusunka.
Kar a turo maka wani Link da sunan ana ba da kyautar kudi ka shiga duk karya ne. Kar kuma su ce ka tura musu wani code (lambobi) da aka turo a layinka ka basu. A kiyaye.
Comments
Post a Comment