#Rahamar Allah (T)
Allah (T) ya so cikin hikimarsa da Rahamarsa ga bayinsa ya tayar masu da mai kira a dai dai lokaci da zamanin da yake da wahalar sha'ani, wannan zamani namu ya dace da sallamawa Jagoranci wanda ya doru akan kira na akoma wa nizamnin musulunci.
Alhamdulillah, cikin yalwar Rahma ta Ubangiji sai ya tayar da wannan mai kiran a nahiyarmu, a kasarmu, a yankinmu. Wannan bawan Allah rashin amsa masa a wannan zamani hasara ce a duniya da rasa fatan lahira. Amsa masa kuwa kubuta ne daga yanayi na rashin tabbas da fatan samun rabon duniya dana lahira.
Rikirkicewar al'amurra, da fasadi a ban kasa, na iya samuwa su cigaba da faruwa sakamakon gangancin rashin taimakawa wannan bawan Allah, hatta dimuwa a kowane irin al'amari za ta iya riskar mutane sakamakon sakaci da hakkin wannan bawan Allah, Allah (T) ka yi mana tagomashi da taimakon wannan bawan Allah a daidai lokaci mai wahalar taimakawa, Allah (T) ka amfanar da mu.
Comments
Post a Comment